Gwamnan Neja ya nada mata 131 a matsayin masu taimaka masa
Gwamnan Jihar Neja dake Najeriya Mohammed Umaru Bago ya nada mata 131 a matsayin wadanda zasu taimaka masa gudanar da ayyukan sa a jihar.
Wallafawa ranar:
Mai magana da yawun sa Bologi Ibrahim yace, daga cikin matan 131 da aka nada, 41 zasu zama masa kodineta a yankunan jihar, yayin da 90 kuma za su rike mukamin manyan masu taimaka masa da ake kira da turanci SSA.
Gwamnan ya bukaci wadanda aka nada da su jajirce wajen bada gudumawa ta hanyar da gwamnatin sa zata samu nasarar sauke nauyin da aka dora mata.
Bago yace nada wadannan tarin mata na daga cikin alkawarin da yayi lokacin yakin neman zabe na bas u damar taka rawa a cikin gwamnatin sa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu