Isa ga babban shafi

Ya kamata gwamnatin Najeriya ta sanya takunkumi ga ‘yan fashin da ke yiwa mata fyade - UNICEF

Wakiliyar Asusun Kula da Kananan Yara ta Majalisar Dinkin Duniya UNICEF a Najeriya, Cristian Munduate, ta bukaci Gwamnatin kasar da ta yi amfani da dokokin da suka dace domin gurfanar da ‘yan fashin da suka aikata ta’asar cin zarafin Bil Adama.

UNICEF ta ce ya kamata a fara daukar matakai masu tsauri kan wadanda ke cin zarafin mata.
UNICEF ta ce ya kamata a fara daukar matakai masu tsauri kan wadanda ke cin zarafin mata. © Thecable
Talla

Cristian ta yi wannan kiran ne a yayin wani taron tattaunawa da manema labarai na shirye-shiryen bikin ranar jin kai ta duniya a birnin Maiduguri.

UNICEF ya yi nuni da cewa, abu ne da ba za a amince da shi ba a ce gwamnatoci ba su dauki tsattsauran mataki ba a kan wadanda suka sace daliban makaranta, da kashe mata da malamai, da kuma yi wa kananan yara mata fyade.

Ta yi kira da a karfafa tsarin shari’a yadda ya kamata, ta kuma yi gargadin a daina wannan aika-aika ta yadda yara za su iya zuwa makarantu ba tare da fargabar sace ko yi musu fyade ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.