Isa ga babban shafi

Kotun Koli a Najeriya ta fara sauraron karar da Atiku ya shigar akan Tinubu

Kotun koli ta fara sauraron karar da babban dan takarar kujerar shugabancin Najeriya na jam’iyar PDP Atiku Abubakar ya shigar bisa dogaro da wasu sabbin hujjoji da ya gabatar akan shugaban kasar Bola Tinubu na jam’iyar APC, domin ganin an soke an soke zaben.

Atiku Abubakar da kuma Peter Obi su ke kan gaba wajen kalubalantar sakamakon zaben, inda su ke neman a soke zaben, saboda zargin an tafka magudi.
Atiku Abubakar da kuma Peter Obi su ke kan gaba wajen kalubalantar sakamakon zaben, inda su ke neman a soke zaben, saboda zargin an tafka magudi. © Daily Trust
Talla

Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriyar ta ayyana Tinubu a matsayin wanda ya lashen zaben ne bayan da ta gudanar da babban zaben kasar a watan fabrairu, abinda yasa babban abokin hamayyar sa, Atiku Abubakar yayi watsi da sakamakon kuma ya shigar a gaban kotu.

Ita kuwa kotun sauraron karakin zabe anata bangaren watsi ta yi da karar da Abubakar Atiku ya shigar da kuma wanda Peter Obi na jam’iyar Labour ya gabatar tare da tabbatarwa Tinubu da nasarar  da ya samu a zabe.

Bisa rashin gamsuwarsa da hukuncin da kotun sauraron korafin zaben tayi, sai Atiku ya garzaya kotun kolin kasar ya shigar da wata karar tare da bukatar a bashi wata dama da zai gabatar  da wasu shaidu da ya ce ya samo akan Tinubu da sukja jibanci batun takardun karatun bogi da ya gabatar.

Ana saran kotun ta kuma saurari karar da Peter Obi da Jam’iyyar APM suka shigar bayan na Atikun.

 

Sai dai wasu bayanai da muka samu da dumudumin su na bayyana cewa kotun ta dage sauraron karar dake kalubalantar nasarar Bola Ahmed Tinubu zaben shugaban kasar zuwa ranar 25 ga watan Fabrairu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.