Isa ga babban shafi

Kotu ta dage haramcin IPOB, ta ce a biya Kanu diyar naira biliyan 8

Alkalin babbar kotun Jahar Enugu a tarayyar Najeriya, mai shari’a A. O. Onovo, ya ce ayyana kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biafra IPOB, da kungiyar gwamnonin yankin kudu masu gabashin kasar ta yi a matsayin haramtatciyar kungiya, ya sabawa kundin tsarin mulkin kasar.

Jagoran kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu.
Jagoran kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu. REUTERS - Afolabi Sotunde
Talla

Idan dai ba a manta ba, a shekarar 2017 ce kungiyar gwamnonin yankin karkashin jagorancin gwamnan Ebonyi David Umahi, ta haramta ayyukan kungiyar, kafin daga bisani gwamnatin tarayyar kasar ta bayyana kungiyar a matsayin ta ta’addanci.

Toh sai dai jagoran kungiyar Nnamdi Kanu, ta hannun lauyansa Aloy Ejimakor sun garzaya kotu don kalubalantar wancan mataki.

Daga cikin bukatun kungiyar a gaban kotu, akwai bukatar ganin an sako jagoransu da warware wancan suna da aka sanya mata, sannan kuma suka nema a baiwa Kanu diyar naira biliyan 8 na bata masa suna da kuma tauye masa hakkinsa na dan kasa.

A hukuncin da mai shari’a Onovo yayi, ya amince da dukkanin bukatun kungiyar ta IPOB, sannan kuma ya bukaci a baiwa Kanu hakuri ta hanyar wallafawa a jaridun kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.