Isa ga babban shafi

Kotun kararrakin zabe ta tabbatar da nasarar gwamna Ahmadu Fintiri na Adamawa

Kotun sauraron kofa-korafen zaben gwamnan jahar Adamawa da ke Arewa maso Gabashin Najeriya, ta yi watsi da karar ‘yar takarar gwamnan jahar karkashin inuwar jam’iyar APC Sanata Aishatu Dahiru Binani ta shigar, don kalubalantar nasarar da gwamna Ahmadu Umaru Fintiri na jam’iyar PDP ya samu.

Gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Fintiri tare da abokiyar hamayyarsa Aishatu Binani.
Gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Fintiri tare da abokiyar hamayyarsa Aishatu Binani. © dailytrust
Talla

A lokacin da jagoran alkalan kotun mai shari’a Theodora Obi Uloho ke yanke hukunci a Asabar din nan, ya ce mai shigar da kara ta gaza wajen tabbatar da zargin saba wa dokokin zabe na shekarar 2022, da  ta ce anyi.

Dama dai Binani ta garzaya kotun ne bisa zargin sabawa dokokin zaben, toh sai dai kotun ta yi watsi da kararta tare da tabbatar da nasarar Fintiri.

A sakamon zaben gwamnan jahar da aka gudanar a farkon wannan shekarar, gwamna Fintiri da yayi wa jam’iyar PDP takara, ya samu kuri’u dubu dari 430, da dari 861, yayin da Binani ta samu kuri’u dubu dari 398, da dari 788.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.