Isa ga babban shafi

An rantsar da Natasha a matsayin sanatar Kogi ta Tsakiya

Shugaban majalisar dattawan Najeriya Godswill Akpabio, ya rantsar da sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, a matsayin sanatar da ke wakiltar Kogi ta tsakiya a zauren majalisar.

Natasha Akpoti-Uduaghan, sanatar da ke wakiltar Kogi ta Tsakaniya a zauren majalisar dattawar Najeriya.
Natasha Akpoti-Uduaghan, sanatar da ke wakiltar Kogi ta Tsakaniya a zauren majalisar dattawar Najeriya. © Daily Trust
Talla

Akawun majalisar Chinedu Akubueze ne ya rantsar da Natasha Akpoti-Uduaghan, a yayin zaman ta na ranar Alhamis nan.

A ranar Litinin din da ta gabata ne dai kotun daukaka kara da ke babban birnin kasar Abuja, ta tabbatar da zaben Natasha, da ta yi wa jam’iyar PDP takarar kujerar sanatan Kogi ta tsakiya a zaben da ya gabata.

Kotun daukaka karar dai, ta yi watsi da karar da sanata Abubakar Ohere ya shigar gabanta, saboda rashin kwarara hujjoji.

Dama dai tun a watan Satumbar daya gabata ne kotun sauraron korafe-korafen bayan zabe a jahar, ta yi watsi da zaben da aka yiwa Ohere na jam’iyar APC tare da tabbatar da Natasha a matsayin wacce ta yi nasarar lashe zaben.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.