Isa ga babban shafi

Kotun daukaka kara ta tabbatar da lashe zaben kujerar sanata da Lalong yayi

Kotun daukaka kara da ke zamanta a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya, ta tabbatar da ministan kwadago da samar da ayyuka na kasar Simon Bako Lalong, a matsayin sanatan da ke wakiltar Filato ta kudu a zauren majalisar dattawar kasar.

Tsohon gwamnan jahar Filato Simon Lalong.
Tsohon gwamnan jahar Filato Simon Lalong. © PLSG
Talla

Kotun dai ta yi watsi da karar dan takarar jam’yar PDP Napoleon Bali ya shigar a gabanta, saboda rashin kwararan hujjoji da ta ce bai da su.

Tun da farko dai, kotun sauraron korafe-korafen zaben Jahar ta ce tsohon gwamnan Jahar ta Filato Lalong ne ya samu nasarar lashe zaben da aka gudanar a ranar 25 ga watan Faburairu wannan shekarar, sakamakon rashin shugabancin a PDP wajen tsaida 'yan takara.

Kotun ta ce, jam’iyar ta yi gaban kanta na rashin mutunta umarnin kotu tun daga matakin gunduma zuwa jaha wajen zaben shugabanni a shekarar 2021, wanda kuma ba su da ikon zaban ‘yan takara.

Alkalan kotun daukaka karar karkashin jagorancin Mai shari’a E.O Williams-Daeoud, sun ce hukuncin da kotun sauraron kararrakin zaben Jahar ta yanke yayi dai-dai.

Jam’iyar PDP dai ta rasa kujeru da dama a kotun sauraron kararrakin zaben jahar, bisa dalilan rashin sahihancin shugannin jam’iyar da suka zabi ‘yan takara a zaben da ya gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.