Isa ga babban shafi
ZABEN GWAMNA

Kotun daukaka kara ta tabbatar da zaben gwamna Abdullahi na Nasarawa

Najeriya – Kotun daukaka kara a Najeriya ta soke hukuncin kotun zaben da ya bayyana David Ombugadu na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya samu nasarar zaben gwamnan jihar Nasarawa, yayin da ta tabbatar da Abdullahi Sule a matsayin zababben gwamna.

Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nassarawa
Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nassarawa © dailytrust
Talla

Alkalan kotun daukaka karan guda 3 sun amince ba tare da hamayya ba, cewar kotun da ta saurari kararrakin zabe a jihar Nasarawa tayi kuskure wajen yanke hukuncin cewar Abdullahi Sule bai samu kuri’u mafi rinjaye ba da zai bashi damar samun nasara.

Saboda haka kotun ta jingine hukuncin kotun zaben, tare da bayyana Abdullahi Sule a matsayin zababben gwamna.

Hukumar zabe a Najeriya ta bayyana gwamna Abdullahi Sule a matsayin wanda ya lashe zaben watan Maris da kuri’u dubu 347 da 209, yayin da David Ombugadu na PDP ya samu kuri’u dubu 283 da 016, abinda ya sa Ombugadu ya ruga kotun zabe domin gabatar da rashin amincewarsa da sakamakon da kuma zargin samun wasu kura kurai lokacin zaben.

Yayin yanke hukunci a kotun zabe, alkalai guda biyu sun baiwa Ombugadu nasara tare da soke zaben Sule, amma alkali guda daga cikin alkalan kotun guda 3 yaki amincewa da matsayin sauran.

Wannan ne dalilin da ya sa gwamna Sule daukaka kara zuwa kotun da ta yanke hukunci a yau.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.