Isa ga babban shafi

Bankin Duniya ya bukaci gwamnatin Najeriya ta soke tallafin mai kacokan

Akwai yiwuwar farashin man fetur ya tashi zuwa naira 750 kan kowanne lita, sakamakon yadda Babban bankin duniya ta bukaci gwamnatin Najeriya ta dakatar da biyan duk wani abu da ya shafi tallafin man fetur.

Wani gidan mai a birnin Lagos na Najeriya.
Wani gidan mai a birnin Lagos na Najeriya. AFP - PIUS UTOMI EKPEI
Talla

Yanzu haka a jahohi irin su Kano da Sokoto ana sayar da man fetur a kan naira 690 yayin da a yankin arewa maso gabashi, a jahohi irin Borno da Yobe a kan naira 700 ake sayar da litar mai.

Tuni ‘yan Najeriya da dama suka ajiye motocinsu gefe guda, saboda matsalar hauhawar farashin man fetur da kuma yadda tsadar rayuwa ta jefa al’umma cikin halin kaka-ni ka- yi.   

Tuni masu sharhi kan harkokin kasa suka yi tir da shawarar Bankin Duniyar, inda suka yi kira ga gwamnatin Najeriya ta gaggauta neman mafita kan matsalolin tattalin arzikin da suka dabaibaye kasar

A watan Satumba wasu kafafen yada labaran Najeriya suka ruwaito cewa duk da alwashin da shugaba Bola Ahmed Tinubu cewa tallafi ya tafi kenan, gwamnatinsa ta ci gaba da biyan tallafi a kan man fetur, inda a watan Agusta ta biya naira biliyan 169 da miliyan dari 4 a kan tallafin.

Wani babban jami’in Bankin Duniya, Alex Sienaert ya tabbatar da cewa gwamnatin Najeriya ta ci gaba da biyan tallafin man fetur a wani jawabi da ya gabatar jiya a Abuja, a game da halin da tattalin arzikin Najeriya ke ciki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.