Isa ga babban shafi

Shell zai janye daga aikin hakar danyen mai a tekun Najeriya

Kamfanin hakar danyen mai na Shell ya bayana aniyar janyewa daga aikin hakar mai a Najeriya, bayan da ya sanar da cewa zai sayar da hannun jarin kamfani hakar danyen man sa na cikin teku, wato Shell Petroleum Development Company of Nigeria Limited a kan kudi dala biliyan 1 da miliyan dari 3.

Tambarin kamfanin Shell.
Tambarin kamfanin Shell. REUTERS - ARND WIEGMANN
Talla

Shell zai sayar da wannan hannun jari ne ga Rennnaisance, wani rukunin kamfanoni 5 masu hakar danyen mai da ke aiki a Najeriya, da wani rukunin kamfanonin makamashi na kasa da kasa.

Wata sanarwa daga kamfanin Shell din ta ce an tsara wannan ciniki ne ta inda ba zai shafi yawa da karfin aikin da ya ke yi ba don amfanin rukunin kamfanonin da zai karbi ragamar tafiyar da shi, biyo bayan sayar da shi.

Da ya ke  tofa albarkacin bakinsa a kan wannan mataki na Shell, wani babban darakta a kamfanin, Zoë Yujnovich, da wannan al’amari, an kai wata gaba mai mahimmanci a kan abin da ya  shafi ayyukan Shell a Najeriya, inda zai karkata  hankalinsa a kan ayyukan da ba sa illa ga muhalli.

Kammala wannan ciniki zai ta’allaka ne da amincewar gwamnatin tarayyar Najeriya da kuma cika wasu sharruda masu mahimmanci.

Rukunin kamfanonin da zai karbi ragamar aikin hakar danyen mai a ciki teku daga hannun Shell ya kunshi kamfanin ND Western, Aradel Energy, First E&P, Waltersmith da Petrolin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.