Isa ga babban shafi

Kuskure ne Tinubu ya ce CBN ya karbe kudaden cinikin da NNPC ke yi - Atiku

Najeriya – Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar ya bayyana umarnin da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bai wa kamfanin man NNPC cewar Babban Bankin kasar na CBN ne zai karbe hurumin kula da kudaden da yake sayar da danyen mai a matsayin haramcaciya.

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar
Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar © premium times
Talla

Sanarwar da Abubakar ya rabawa manema labarai tace wannan umarni na Tinubu ya ci karo da 'yancin da doka ta bai wa NNPC na gudanar da ayyukan sa, a matsayinsa na kamfani mai zaman kansa dauke da hannayen zuba jarin 'yan kasuwa.

Tsohon mataimakin shugaban yace ba daidai bane Tinubu ya umarci NNPC ya dinga gabatar da rasitan cinikin danyan man da ya yi, domin a halin yanzu dokar dake kula da kamfanin ya kawar da shi daga karkashin gwamnati.

Abubakar yace matakin ya zama katsalandan a harkokin kamfanin man sabanin abinda dokar gudanar da shi ya tanada.

Sabon tambarin kamfanin kula da albarkatun man Najeriya NNPC da gwamnati ta saida wa 'yan kasuwa.
Sabon tambarin kamfanin kula da albarkatun man Najeriya NNPC da gwamnati ta saida wa 'yan kasuwa. REUTERS - AFOLABI SOTUNDE

Tsohon mataimakin shugaban kasar yace daukar irin wannan mataki ka iya jefa shakku ga masu sha'awar zuwa Najeriya zuba jari.

Sai dai bangaren gwamnati na cewa wannan matsayi na shugaban kasa zai bada damar kawar da shakku dangane da yadda kamfanin ke aiki da kuma tabbatar da gaskiya.

Masana na kallon wannan kamfani a matsayin kashin bayan tattalin arzikin Najeriya ganin yadda kasar ta dogara da shi wajen samun kudaden ketare ta hanyar sayar da 'danyen man fetur a kasuwannin duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.