Isa ga babban shafi

‘Yan bindiga a Najeriya sun kashe mutane shida da suka hada da ‘yan sanda hudu a Ebonyi

A Najeriya,wasu ‘yan bindiga da ake zargi da kasancewa cikin kungiyar ‘yan aware sun kashe mutane shida da suka hada da ‘yan sanda hudu a jihar Ebonyi da ke kudu maso gabashin kasar, kamar yadda ‘yan sanda suka sanar.

Wasu 'yan kungiyar IPOB masu fafutukar kafa kasar Biafra.
Wasu 'yan kungiyar IPOB masu fafutukar kafa kasar Biafra. http://naijagists.com
Talla

An kai harin ne da sanyin safiyar Juma’a a kusa da shingen binciken ‘yan sanda da ke kan titin da ke kusa da birnin Abakaliki, in ji kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Joshua Ukandu.

Jagoran kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu.
Jagoran kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu. REUTERS - Afolabi Sotunde

Jami’in ya kara da cewa an fara harbe-harbe inda jami'ai hudu suka mutu sannan wasu fararen hula biyu suka mutu a rikicin.

Batun neman cin gashin kai da wasu kungiyoyi ke ikirari tsawon shekaru na ci gaba da haifar da tashin hankali a wasu yankunan kasar,yanzu haka wasu daga cikin kabilun kasar  musamman Igbo a shekarar 1967 suka ayyana kasar Biafra mai cin gashin kanta ,matsalar da ta haifar da yakin basasa na shekaru uku da ya yi sanadin mutuwar sama da mutane miliyan guda.

Wasu daga cikin magoya bayan kungiyar IPOB a birnin Aba. 28 ga watan Mayu, 2017.
Wasu daga cikin magoya bayan kungiyar IPOB a birnin Aba. 28 ga watan Mayu, 2017. STEFAN HEUNIS / AFP

Rikicin da ake fama da shi a yankin kudu maso gabashin kasar mai fama da rikicin ‘yan awaren da aka gada daga yakin Biafra, na daya daga cikin kalubalen tsaron da shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ke fuskanta, yayin da dakarun kasar ke fafatawa da kungiyoyin ‘yan bindiga a jihohin arewa maso yamma.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.