Isa ga babban shafi

'Dan Ganduje ya jinjinawa aikin hukumar yaki da rashawa ta Kano

Najeriya – Abdulaziz Ganduje, wanda 'da ne ga tsohon gwamnan jihar Kano dake Najeriya, wato Abdullahi Umar Ganduje, ya kai ziyara ga shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano, Muhiyi Rimingado domin jinjina masa a kan aikin da yake gudanarwa.

Abdulazeez Ganduje lokacin da ya ziyarci shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano,Muhuyi Rimingado
Abdulazeez Ganduje lokacin da ya ziyarci shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano,Muhuyi Rimingado © Daily Nigerian
Talla

Jaridar Daily Nigerian da ake wallafawa a Najeriya ta ruwaito cewar, Abdulaziz ya kai ziyarar ce domin yabawa Rimingado a kan kokarin sa tare da goyan bayan tuhumar da ake yiwa mahaifinsa Ganduje da uwargidansa, wadda ke mahaifiya ga shi (Abdulaziz) da kuma 'dan uwansa.

Daily Nigerian tace bayanai masu sahihancin da ta samu sun shaida mata cewar, bayan yabawa da tuhumar da ake yiwa iyayen na sa, ya kuma bayyana damuwa a kan yadda aka cire sunan sa ba bisa ka'ida ba a matsayin darakta daga daya daga cikin kamfanonin da ake kara bada sanin sa ba.

A korafin da ya gabatar, Abdulaziz ya bayyana cewar wani mai harkar gine gine ya tintibe shi domin taimaka masa sayen filaye a Kano tare da masa tayin dubban daloli da kuma kamisho na naira miliyan 35.

Jaridar tace shi Abdulaziz ya mika kudaden da aka canja zuwa daloli ga mahaifiyarsa, amma abin takaici bayan wata 3 sai wanda ya biya kudin ya gano cewar an sayarwa wasu mutane daban filayen, saboda haka ya bukaci a mayar masa da kudaden sa.

Tuni dai hukumar yaki da cin hanci da rashawa a Kano ta gurfanar da tsohon gwamnan da uwargidansa Hafsat da 'dan su Umar Abdullahi Umar da kuma wasu mutane 5 da ake tuhuma da laifuffuka guda 8 da suka shafi cin hanci da rashawa da kuma karkata dukiyar jama'a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.