Isa ga babban shafi
Libya-Nijar

Libya na mayar da baki 'yan kasashen ketare gida

Kasar Libya ta kwashe baki ‘yan kasashen waje kusan 200 da ake tsare da su a kasar zuwa Jamhuriyar Nijar.

Libya na mayar da baki 'yan kasashen waje Nijar
Libya na mayar da baki 'yan kasashen waje Nijar AFP PHOTO / MARIO LAPORTA
Talla

Rahotanni sun ce, an kwashe bakin ne daga filin jirgin saman Mitiga da ke Gabashin Tripoli a karkashin sa idon hukumar kula da kaurar mutane ta duniya.

Kwashe bakin hauren zuwa kasashen su na daga cikin manufofin hukumomin da ke iko da kasar Libya, wadanda ke ci gaba da tare daruruwan baki 'yan kasashen waje yanzu haka.

Hosni Abu Ayana, mai Magana da yawun ofishin da ke kula da bakin hauren, ya ce cikin wadanda aka kwashe zuwa Nijar sun hada da mata 50 da yara guda 4.

Jami’in ya ce yanzu haka akwai baki 900 da ake saran kwashe su daga kasar a cikin makwanni masu zuwa.

Hukumar kula da 'yan masu kaura ta duniya ta ce yanzu haka ta taimakawa baki 1,589 da ke nema ficewa daga Libya dan komawa kasahsen su.

Rahotanni sun ce masu safarar mutane na amfani da tashin hankalin Libya wajen yaudarar mutane suna kai su kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.