Isa ga babban shafi
Libya

Jamian tsaron gaban ruwan Libya sun ceto bakin haure 120

Masu gadin gaban teku a kasar Libya sun yi nasarar ceto wasu bakin haure akalla 120 da kwale-kwaken su ya sami matsala a tsakiyar teku yau lahadi.

Jirgin ruwan wasu bakin haure da ya fadi kafin masu aikin ceto su ceto su.
Jirgin ruwan wasu bakin haure da ya fadi kafin masu aikin ceto su ceto su. Marina Militare/Handout via REUTERS
Talla

Tun juma'a ne dai bakin haure suka tashi daga garin Sabratha dake da nisan kilomita 70 daga birnin Tripoli, amma kuma suna cikin tafiya kwale-kwalen na su ya sami matsala.

Bayanai na nuna bakin hauren sun fito ne daga kasashe daban-daban na nahiyar Africa.

Koda a jiya Asabar Hukumomin kasar Libya sun bayyana cewa sun kama bakin haure 400 dake neman tsallakawa turai ta teku.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.