Isa ga babban shafi
Nijar

‘Yan takara 41 ne ke neman shugabancin Jmahuriyar Nijar

A Jamhuriyar Nijar, ‘yan takara 41 ne suka gabatar da takardunsu na takarar shugabancin kasar ga ma’aikatar cikin gida.

Mahamadou Issoufou, shugaban kasar Nijar mai ci.
Mahamadou Issoufou, shugaban kasar Nijar mai ci. ©RFI
Talla

Wannan ne karon farko da ake samun wannan adadi na ‘yan takara gabanin zaben shugaban kasar mai zuwa a ranar 27 ga watan Disamba. A zaben da ya gabata, ‘yan takara 16 ne suka nemi darewa kujerar shuganacin kasar.

Idan wa’adin shugaba Mahamadou Issoufou ya zo karshe, zai kasance shugaba na farko da ya mika mulki ga farar hula; wata dga wata gwamnatin farar hula, zuwa ta farar hula.

Dukkannin masu fada a ji a siyasar Nijar su na cikin wadannan ‘yan takara da suka 41 da suka gabatar bda takardun takararsu.

Daga cikin su akwai tsohon shugaban kasar Mahamane Ousmane, Seyni Oumarou, Bazoum Mohamed, Janar Salou Djibo, Hama Amadou, Albadé Abouba da Sheikh Boureima Daouda, babban limamin masallacin jami’ar Yamai.

Hukumar zaben kasar Ceni ta ce masu zabe miliyan 7 da dubu dari 4 ne suka yi rajistan kada kuri’a a zaben da ke tafe a watan Disamba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.