Isa ga babban shafi
Nijar - Ta'addanci

Adadin wadanda suka mutu a harin ta'addancin Nijar ya kai 141

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta ce adadin mutanen da suka mutu sakamakon harin 'yan ta’adda a makon jiya ya tashi zuwa 141 daga 137 da aka sanar, kuma shine mafi muni da kasar ta taba gani.

An tura sojoji na musamman a yakin da 'yan bindigan suka yi aika-aikar a Nijar.
An tura sojoji na musamman a yakin da 'yan bindigan suka yi aika-aikar a Nijar. MICHELE CATTANI / AFP
Talla

Ministan cikin gida Alkache Alhada da ya ziyarci daya daga cikin kauyukan da aka kai harin ya ce sun gana da mutanen kauyen da aka kai harin da ya ritsa da mata da maza da kuma yara kanana.

Alhada ya yi gargadin cewar hare-haren na iya haifar da mummunar tashin hankali tsakanin jama’ar da ke zama a yankin.

Hukumar kula da kananan yara t a UNICEF ta ce daga cikin wadanda aka kashe har da yara 22 masu shekaru tsakanin 5 zuwa 17, yayin da wasu da dama kuma suka rasa iyayen su.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.