Isa ga babban shafi
Nijar-Mata

Wahalar Algeria ta tilasta wa matan Nijar rungumar sana'a a gida

Yankin Kance da ke cikin jihar Damagaram a Jamhuriyar Nijar ya yi kaurin-suna a game da yadda mata ke tafiya ci rani a kasar Algeria. Sau da dama, mahukuntan Algeria na taso keyar wadannan mata a cikin yanayi na kunci zuwa kasarsu ta asali.

Matan Afrika na shan wahala a kan hanyarsu ta zuwa ci-rani a wasu kasashen duniya, inda a wasu lokuta suke rasa rayukansu
Matan Afrika na shan wahala a kan hanyarsu ta zuwa ci-rani a wasu kasashen duniya, inda a wasu lokuta suke rasa rayukansu Reuters/Afolabi Sotunde
Talla

Sai dai a yanzu, matan sun fara rungumar kananan sana'o'i a Nijar, abin da ke hana su yin tafiye-tafiyen a yanzu.

Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakken rahoton Ibrahim Malam Tchillo daga Damagaram

 

03:02

Wahalar Algeria ta sanya matan Nijar rungumar sana'a

 

Matan sun shaida wa RFI Hausa cewa, daga cikin kananan sana'o'in da suka ruguma har da sayar da kayan lambu, abin da ke ba su damar dogaro da kansu a gida ba tare da tunanin zuwa wata kasa kamar Algeria ba don neman arziki.

Salma Yakubu, ita ce jagorar matan da ke sayar da dankalin turawa a kasuwar Matamaye ta kuma bayyana cewa:

Kowa kasn shi ya waye, gwamma mutun ya nemi arziki a gida a maimakon tsallakawa kasar waje   

Malama  Aisha Habou daya daga cikin matan rugagen Rurori da ke sayo kayan lambun daga garake ta kawo cikin gari, ta ce wannan  sana’ar ta fiye mata tafiya ci rani mai cike da kila wa kala na ko ka samo ko ka mutu a hanya.

Karamar sana'armu na biya mana bukata, Allah ya sanya albarka. Inji Aisha Habou 

Sahura Ali wata matashiyar mai jin karfi a jikinta wadda ire-irenta ne ke tafiya ci rani  Algeria amma  a bana, ta rungumi sana’ar kayan lambu. A cewarta:

Daga mu har mazanmu muna amfana da wannan sana'ar a cikin gida.

Tuni manoma a Jamhuriyar Nijar suka bayyana farin cikinsu kan yadda matan ke sayen kayayyakinsu, abin da masana ke cewa, na taka rawar gani wajen bunkasa tattalin arzikin wani bangare na al'ummar kasar.

Hatta hukumomin yankin sun yaba da matakin da matan suka dauka na rungumar kananan sana'o'i maimakon tafiye-tafiyen ci rani mai hadari.

Alhaji Habu Abdo, Magajin Garin Commune Kin Matamaye cewa ya yi:

Yanzu hankalinmu a kwance suke saboda yadda matan ke zama a gida a maimakon daukar kasadar tafiye-tafiye masu hadari

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.