An nada sabon Firaminista a jamhuriyar Nijar
Sabon Shugaban kasar Jamhuriyar Nijar Bazoum Mohammed ya nada Ouhoumadou Mahamadou a matsayin Firaministan da zai jagoranci gwamnatin kasar.
Wallafawa ranar:
Sanarwar da fadar shugaban kasa ta gabatar tace sabon shugaban ya sanya hannu kan dokar nada tsohon Babban Hafsa a fadar shugaban kasa a matsayin Firaministan wanda zai kafa gwamnati nan bada dadewa ba.
Sabon Firaministan ya lashe zaben Majalisar dokoki a bara kuma ya taba rike mukamin ministan makamashi da ma’adinai da masana’antu tsakanin shekarar 1991 zuwa 1993, yayin da yayi ministan kudi tsakanin shekarar 2011 zuwa 2012.
Firaministan na daga cikin makusantar tsohon shugaban kasa Mahamadou Issofou kuma yana da karfin fada aji a Jam’iyar PNDS Tarayya mai mulkin kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu