Bankin AfDB zai kashe Dala biliyan 6 da rabi a Nijar
Bankin Raya kasashen Afirka na AfDB ya bayyana cewar zai kashe Dala biliyan 6 da rabi a Jamhuriyar Nijar wajen ayyukan da suka shafi noma da samar da makamashi da kuma gina kayan more rayuwa.
Wallafawa ranar:
Shugaban Bankin Akinwumi Adeshina ya bayyana haka yayin ganawa da shugaban Nijar Bazoum Mohammed a wajen taron sauyin yanayin dake gudana a Glasgow.
Adeshina ya bayyana aikin gina hanyar motar Tamaske da ta ratsa Nijar a matsayin mai matukar muhimmanci ga Bankin saboda yadda zata taimaka wajen sada jama’a da kuma saukaka zirga zirga.
Shugaban Bankin ya kuma bayyana kafa wani asusu na musamman da za’ayi amfani da shi wajen taimakawa sana’oin mata da matasa a Afirka.
Shugaban Nijar Bazoum Mohammed ya nemi karin tallafi a bangaren koyar da sana’oi da kuma samar da hanyoyin sadarwa na zamani.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu