Nijar-Mata
Shirin kare lafiyar mata da kuma takaita haihuwa a Nijar
Kamar sauran kasashe na yammacin Afrika da suka yi baki guda don cimma daya daga muradun karni ta fannin kare lafiyar mata da yara kanana, Jamhuriyar Nijar ta kaddamar da wata sabuwar siyasa da ke kunshe da manyan dubaru da za su sauya alkalumman da ke nuna kasar a matsayin wadda mata suka fi yawan haihuwa a duniya. Alkalumma dai na nuni da cewa kowace mace daya na haihuwar akalla ‘ya'ya 7 a rayuwarta. Wakilinmu na Damagaram Ibrahim Malam Tchillo na dauke da rahoto a kai.
Wallafawa ranar:
Kunna - 03:16