Isa ga babban shafi
Nijar

An kama jami'in gwamnatin Nijar dauke da hodar iblis

Rundunar 'Yan sanda a jihar Agadas da ke arewacin Jamhuriyar Nijar ta tsare shugaban Karamar Hukumar Fashi tare da direbansa  bayan gano kilogram fiye da 200 na hodar ibilis a cikin motarsa a ranar Lahadin da ta wuce a wani  wurin binciken jami'an tsaro.

Jami'an 'yan sandan jamhuriyar Nijar
Jami'an 'yan sandan jamhuriyar Nijar © AFP
Talla

Wasu shaidu sun ce sung a jami'an hukumar na binciken wasu motoci kirar Toyota 4×4 da suka nuna matukar shakku kan kayayin da suke dauke da su duk da dagewar wani mai mukamin kansila da ya so ya kawo tarnaki a aikin jami'an da ke binciken.

Bayan kusa da sa a daya jami'an hukumar suka tabbatar da abin da suke zargi,wato wasu harantatun  abubuwan da aka saka a cikin manyan akwatina wadanda aka yi anfani da motar iko wajan jigilar su.

An dai kiyasta cewa, darajar kwayar ta kai biliyan 5 na kudin CFA.

Ya zuwa yanzu hukumomin' 'yan sanda na tsare  da Sharou Sanda, shugaban Karamar Hukumar Fachi tare da matukinsa, yayin da ake ci gaba da neman wani mutun guda da ya hada baki da su, mutunen  da bayanai ke nuna cewar kodawane lokaci za'a iya tasa keyarsu zuwa birnin Yamai.

Ko a ranar 7 ga watan Disamban 2021,sai da Hukumar Yaki da sha da kuma ta'ammuli da muggan kwayoyi ta yi kamen akalla kilogram 330 na  wiwi  tareda tsare mutun 10.

Tun bayan faduwar mulkin tsofon shugaban kasar Libiya Mouammar Khadafi, wani bangare na Saharar Agadas da ke arewacin Jamhuriya Nijar ya zama wanin yankin da masu fataucin muggan kwayoyi da makamai ke cin karansu ba babbaka ,duk da kokarin hukumomin kasar na tabbatar da tsaro a wannan yankin wanda ya raba iyaka da kasashen Libiya da Algeria da kuma Chadi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.