Isa ga babban shafi
Nijar-UNICEF

UNICEF ta koka da karuwar dabi'ar yi wa mata kaciya a Nijar

Yiwa mata kaciya na ci gaba da zama babbar matsala a fanin kiyon lafiyar al’umma, diyaucinsu da kuma take hakkokinsu da ake yi ta wannan mummnar al’ada, lura da irin  aika aikar da ahakan ke haifarwa ga koshin lafiyarsu, Sai dai abin bakin ciki a Jamhuriyar Nijer wannan dabi’a maimakon raguwa sai ci gaba da karuwa a cewar UNICEF.

Alkaluman UNICEF ya nuna karuwar wannan dabi'a a gabashin Jamhuriyyar Nijar.
Alkaluman UNICEF ya nuna karuwar wannan dabi'a a gabashin Jamhuriyyar Nijar. Carine Frenk/RFI
Talla

Haka dai abin ya ke, idan ba a dau matakan da suka dace ba yan mata miliyan 68 ne za su fuskanci kaciyar nan da shekara ta 2030 a duniya, kamar yadda wani bincike da hukumar yara ta Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya nunar.

Ranar yaki da yi wa mata kaciya da ake guddanarwa a ko wace a ranar 6 ga wannan wata na fabrairu a ko ina cikin duniya  na nuna bukatar daukar ingantatun matakan yaki da al’adar kaciyar da ke zama cin zarafi tare da take babban hakkin  ya mace a duniya.

A cikin yankunan karkararar jamhuriyar Nijer, musaman a yankin yammacinta kashi  75.7% na matan da suka kama daga shekaru 15 zuwa 49 da haihuwa ne ake yi wa kaciya mafi yawansu kuma ana yi masu ne tun suna yan shekaru 5 zuwa 8 da haihuwa a cewar rayhoton na UNICEF.

Irin wannan kaciya ta yanke wani sashen matuntakar ya mace an fi yin ta ne a yankin gabashin kasar ta Nijer. Haka kuma kashi, 80% na kaciyar ana yinta ne da asaken gargajiya.

Domin ganin an dakatar da wannan mummunar al’ada, gwamnati da abukan huldarta na ci gaba da kara kaimi wajen wayar da kanun al’umma.

Kadidiatou Abdoulaye Idani, shugabar kungiyar matasa yan mata ta fannin kiyon lafiyar haihuwa (AJFSR) ta bayyana bakin cikinta kan yadda ake ci gaba da samun yi wa mata kaciyar, musaman  a yankunan karkara, inda sannu a hankali ta ke ci gaba da zama wani abin yayi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.