Isa ga babban shafi

Sojojin Nijar da na Barkhane sun kai hareharen hadin gwiwa sau 15

Rundunar sojin Jamhuriyar Nijar ta sanar da cewar sau 15 take gudanar da sintiri da samamen hadin gwiwa tsakanin ta da rundunar sojin Faransa ta Barkhane a iyakar kasar da Mali domin kakkabe ‘Yan ta’addan da suka addabi yankin.

Dakarun Barkhane da na Nijar
Dakarun Barkhane da na Nijar AP
Talla

Babban hafsan tsaron Nijar Janar Salifou Modi ya sanar da wannan aiki da aka yiwa suna ‘Operaton Almahaou’ wanda aka gudanar tsakanin watan Yuli zuwa Oktoban wannnan shekara.

Sanarwar da rundunar ta gabatar tace an kammala wannan sintirin da aka shirya ne a wannan mako mai karewa, kuma Janar Modi ya sanya ido akai tare da abokan aikin su na rundunar Barkhane ta Faransa.

Sojojin sun ce aikin ya basu damar murkushe shirin kai hare hare da dama da yan ta’adda suka shiya da lalata kayan yakin su tare da kwace wasu taron makamai da kuma kama mutane akalla 30 da ake zargi.

Sojojin sun ce aikin ya basu damar samar da kwanciyar hankali da kuma natsuwa ga manoman dake aiki a yankin tare da makiyaya domin ci gaba da aikin samar da abinci da kuma kula da lafiyarsu.

Janar Modi ya jinjinawa dakarun akan nasarar da suka samu da kuma hadin kann da akayi tsakanin bangarorin guda biyu.

Jamhuriyar Nijar na fama da Yan ta’addan dake kai mata hari daga kasashen dake makotaka da ita musamman Mali da Buurkina Faso da kuma Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.