Isa ga babban shafi

Harin kwanton bauna ya halaka sojojin Nijar biyar

Akalla sojojin Nijar 5 sun mutu ya yin da wasu 4 suka samu raunuka a wani harin da 'yan bindiga dauke da makamai suka kai wa ayarin motocin su ranar Lahadi, kan hanyar Tabaraga-Arlit kusan kilomita 300 daga Aagadas. 

Wasu sojojin jamhuriyar Nijar da ke taimakawa Najeriya wajen yaki da kungiyar Boko Haram.
Wasu sojojin jamhuriyar Nijar da ke taimakawa Najeriya wajen yaki da kungiyar Boko Haram. AFP - PHILIPPE DESMAZES
Talla

Jamhuriyar Nijar dai na daga cikin kasashen yankin Sahel, da ke fama da hare-haren masu tayar da kayar baya da suka addabi kasar.

Tuni akayi jana'izar sojojin da suka mutu yau da safe  bisa jagorancin shugaban hafsan sojojin kasar a garin Arlit. 

Shiga alamar sauti domin sauraron cikakken rahoton da oumarou Sani ya hada daga Nijar din.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.