Sana'ar sayar da fatar rago ba ta yi armashi ba a bana a Nijar
Babbar hada-hadar da ta fi jan hankalin jama'a bayan babbar salla a kowace shekara ita ce harakar fata da kirgin dabbobin da aka yi layya da su, saboda harka ce mai samar da kudi masu yawa ga masu yin ta a irin wannan lokaci.
Wallafawa ranar:
Kunna
Tun bayan durkushewar kamfanonin sarrafa fata na cikin kasa, 'yan kasuwar Najeriya ke saye mafi yawan fatar da ake samarwa a Nijar.
To sai dai a bana saboda faduwar darajar naira, farashin fatar ya fadi warwas inda har ta kai masu harkar fatar na fargaba.
Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakken rahoton Wakilinmu na Damagaram Ibrahim Malam Tchilo
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu