Isa ga babban shafi

Aljeriya ta kora dubban 'yan ci-ranin Nijar zuwa kasashensu

Rahotanni daga Jamhuriyar Nijar sun ce ‘yan ci-rani fiye da dubu biyu ne suka isa garin Agadez da ke Arewacin kasar, bayan da mahukuntan Aljeriya suka tasa keyarsu. 

Wasu 'yan ci-rani a cikin Sahara
Wasu 'yan ci-rani a cikin Sahara ASSOCIATED PRESS - Lefteris Pitarakis
Talla

Duk da cewa akwai ‘yan kasar ta Nijar a cikin wannan ayari, amma mafi yawansu sun fito ne daga kasashen Afirka da ke Yankin Kudu da Sahara, wanda suka shiga kasar ta Aljeriya ba a kan ka’ida ba. 

Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakken rahoto tare da Shamsiyya Haruna 

Wasu daga cikin 'yan ci-ranin shaida wa RFI Hausa irin bakar ukubar da suka sha a hannun jami'an tsaron Aljeriya kafin daga bisani a tasa keyarsu zuwa Agadez.

Hukumar da ke kaarbar ‘yan Nijar da aka koro daga wata kasa, ta ce dukannin ‘yan ci-ranin su dubu 1 da 800 da Aljeriya ta tasa  keyarsu, na samun kulawar da ta dace, kodayake mafi yawansu na cikin damuwa. 

La’akari da yadda ake samun karuwar kwarara bakin hauren, Hukumar Kula da Kaurar Jama’a ta Majalisar Dinkin Duniya IOM, ta bullo da wani shirin wayar da kawunan ‘yan ci-rani kan muhimmanci yin balaguro a kan ka’ida. 

Hukumomi a Agadas sun ce a halin da ake ciki, akwai bakin haure dubu 5 zuwa 7 a jihar da ake nema wa mafita tare da sauran abokan hulda. 

A kwanakin da suka gabata, Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci sojojin da suka kwace mulki a Jamhuriyar Nijar da su bayar da dama a shigar da kayan agaji domin tallafa wa dinbin ‘yan cii-rani da kuma ‘yan gudun hijirar da ke rayuwa a sansanoni daban daban da ke cikin kasar. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.