Isa ga babban shafi

Sojojin Nijar sun sanar da dakile yunkurin Bazoum na tserewa zuwa Najeriya

Gwamnatin mulkin sojin Nijar ta sanar da dakile wani yunkurin hambararren shugaban kasar Mohamed Bazoum na tserewa daga gidan da ake tsare da shi a wannan Alhamis tare da iyalansa.

Hambarerren shugaban jamhuriyar Nijar, Mohamed Bazoum.02/05/22
Hambarerren shugaban jamhuriyar Nijar, Mohamed Bazoum.02/05/22 AFP - ISSOUF SANOGO
Talla

Kakakin gwamnatin sojin Nijar, Kanar-Manjo Amadou Abdramane, wanda ya bayyana hakan cikin jawabin da ya yi wa jama’ar kasar ta Talabijin, da kuma wanda aka wallafa a shafukan sada zumunta ya ce Bazoum da iyalinsa sun tsara guduwa daga fadar shugaban kasar ne da misalin karfe uku na dare.

Jami’in ya ce hambararren shugaban kasar Mohamed Bazoum ya yi kokarin tserewa tare da iyalansa da masu dafa masu Abinci 2 da kuma jami’an tsaro guda 2.

Shirin shiga Najeriya

Kanar-Manjo Amadou Abdramane ya ce ‘’matakin farko na wannan shiri shine na su fice daga cikin fadar zuwa kewayen wurin inda wata mota ke jiransu daga nan ne za a dauke su zuwa wani gida da ke cikin unguwar Tchangareya, daga nan kuma a nufi wani wuri inda wasu jirage biyu masu saukar ungulu na wata kasar waje za su kai su Birnin Kebbi da ke tarrayar Nijeriya’

Sanarwar sojojin ta kuma jinjinawa sojojin da hazakarsu wajen dakile wannan yunkurin tare da kare rayuka.

Juyin Mulki

Shugaba Mohamed Bazoum dai ya kasance tsare tun bayan da jami'an tsaron fadarsa suka kifar da gwamnatinsa suke kuma cigaba da yin garkuwa da shi tun karshen watan Yuli.

Lamarin ya yi sanadiyyar raba gari tsakanin kasar ta Nijar da uwargijiyarta Faransa ta hanyar korar jakadanta da kuma sojojinta 1500 da ke yaki da kungiyoyin masu da’awar jihadi a yankin Sahel musaman a yankin iyakoki 3.

Kaddamar da bincike

Tuni mahukuntan sojin suka sanar da kama wadanda aka zargi da kissa shirin tsarewar Bazoum, bayan tare da kaddamar da bincike.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.