Isa ga babban shafi

Nijar ta janye daga aikin hadin gwiwa na yakar ta'addanci a yankin Tafkin Chadi

Rahotanni na nuni da cewa Jamhuriyar Nijar ta janye daga rundunar hadin gwiwa da ke yaki da ta’addanci a yankuna Tafkin Chadi, wadda ta kunshi kasashen da suka hada da Najeriya, Kamaru, Chadi da Jamhuriyar  Benin, lamarin da ya  kasance tamkar babban koma-baya ga kokarin kakkabe ‘yan ta’adda.

Wasu dakarun Sojin Nijar.
Wasu dakarun Sojin Nijar. ISSOUF SANOGO / AFP
Talla

Rahoton da jaridar ‘Daliy Trust’ da ake wallafawa a Najeriya ta yi ya danganta janyewar Nijar daga wannan gagarumin aiki da takunkuman da aka lafta wa gwamnatin mulkin sojin kasar, sakamakon juyin mulki da  sojoji suka yi.

A watan Yulin wannan shekarar ne sojoji suka kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum na Jamhuriyar Nijar, lamarin da ya janyo suka daga sassan duniya, musamman ma daga ECOWAS, abin  da ya sa kungiyar ta kasashen Yammacin Afrika ta kakaba wa Nijar takunkuman karayar tattalin arziki har ma da dakatar da ita daga kungiyar.

Wasu majiyoyi daga yankin Geidam sun ce Jamhuriyar Nijar ta kwashe sojojin da ta jibge a  kan iyakar Najeriya da Nijar, dalilin da ya sa kenan aka samu karuwar hare-hare na Boko Haram a yankunan Malam Fatori, Damasak da Geidam.

A shekarar  2014 aka kafa wannan runduna ta hadin gwiwa ce don yakaar ayyukan ta’addanci da ‘yan ta’adda  ke yi  a yankin Tafkin Chadi, inda aka sake fasalinta tare da kara dakarun cikinta zuwa dubu 10 a shekarar 2015.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.