Isa ga babban shafi

EU ta koka da matakin Nijar na soke dokar haramcin safarar bakin haure

Hukumar gudanarwar kungiyar tarayyar Turai ta bayyana matukar damuwa da matakin da sojojin da ke mulki a jamhuriyyar Nijar suka dauka wajen soke dokar da ta haramta safarar bakin haure daga cikin kasar zuwa Turai ta hanyar ratsa sahara mai cike da hadari.

Wasu tarin bakin haure a Assamaka ta jamhuriyyar Nijar a kokarinsu na ratsa sahara zuwa Turai.
Wasu tarin bakin haure a Assamaka ta jamhuriyyar Nijar a kokarinsu na ratsa sahara zuwa Turai. AFP - STANISLAS POYET
Talla

Tun shekaru 8 da suka gabata ne gwamnatin farar hula a Nijar ta kulla yarjejeniya da kungiyar tarayyar Turai ta yadda kasar ta yammacin Afrika ke karbar makuden kudade wajen kange bakin hauren da ke ratsa kasar zuwa Turai.

Wannan yarjejeniya tsakanin EU da Nijar ta taimaka wajen kange tarin kungiyoyin da ke safarar baki zuwa Turai ta hanyar ratsa sahara mai cike da hadari da kuma teku, wanda a lokuta da dama ake tafka asarar rayuka.

Ficewar Nijar daga wannan yarjejeniya ko kuma janye dokar hana safarar bakin haure kai tsaye hakan na nufin masu balaguro zuwa Turai ta hanyar mai cike da hadari za su dawo ci gaba da hada-hadarsu.

Kwamishiniyar cikin gida ta EU Ylva Johannsson ta ce akwai fargabar wannan mataki na Nijar ya bai wa tarin ‘yan Afrika da ke son ficewa daga kasashensu damar bi ta cikin kasar don kai wa gabar teku.

A cewar jami’ar wannan tafiya ce da ke tattare da hadarin gaske kuma ta ke haddasa asarar tarin rayuka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.