Gombe ta samar da gandun dajin da zai iya daukar shanu miliyan 2
Wallafawa ranar:
Kunna - 04:03
Yayin da Fulani makiyaya ke fama da tsangwama a wasu sassan Najeriya, gwamnatin jihar Gombe ta ware Gandun Dajin da ake kira 'Wawazange' mai daukar shanu miliyan 2, domin tsugunar da makiyayan.
Bayanai sun ce tuni aka fara aikin samar da abubuwan da makiyayan ke bukata irin su madatsar ruwa da asibitocin dabbobi da shuka ciyawa ta zamani domin ciyar dasu.
Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da kwamishinan kula da ayyukan noma na jihar ta Gombe Alhaji Muhammadu Magaji, wanda ya ce suna daukar duk matakan da suka dace wajen inganta noma da kiwo, bayan kaddamar da shirin huji da aka fara yiwa shannun dake Jihar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu