Duniya ta yi watsi da kasashe 10 da suka fi fama da rikici a Afirka - NRC
Wallafawa ranar:
Kunna - 02:39
Wani rahoto da kungiyar da ke kula da ‘yan gudun hijira ta Kasar Norway NRC ta fitar, ya ce duniya ta yi watsi da wasu kasashen Afrika da rikici ya daidaita, wadanda a sanadiyar haka mutane da dama suka zama ‘yan gudun hijira, bayaga matsananciyar yunwa da mace-mace da ta addabe su.
Cikin rahotan da Kungiyar ta fitar ranar Laraba, shugabanta Jan Egeland ya ce, sakamakon halin da ake ciki yanzu haka na Yakin Ukraine, Yankin Afrika zai cigaba da fadawa matsalolin da suka wuce tunanin kowa.
A zantawarsa da Ahmed Abba kakakin kungiyar dake kula da yankin Tsakiya da Yammacin Afirka Tom Peyre - Costa, ya fara da bayyana kasashen da lamarin yafi shafa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu