Colombia
‘Yan tawaye da Gwamnatin Colombia za su gana a Norway
Wakilan Gwamnatin kasar Colombia, da ‘Yan Tawayen kungiyar FARC, sun isa kasar Norway, don fara tattaunawa kan tashin hankalin da aka kwashe shekaru 50 ana yi a cikin kasar. Mai shiga tsakani a taron, Humberto de la Calle, yace duk da yake baya so ya kururuta taron, yana da fata mai kyau cewar, taron zai cim ma nasara.
Wallafawa ranar:
Talla
Babu dai wani bayani dangane da jadawalin taron. Amma wannan ne karon Farko da Gwamnatin kasar za ta fara zaunawa a teburin sasantawa da ‘Yan tawayen a birnin Oslo kafin karo na biyu su sake tattaunawa a Cuba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu