Isa ga babban shafi
Colombia

An fara taron sasanta rikicin Colombiya a Norway

WAKILAN Gwamnatin kasar Colombia da na kungiyar Yan Tawayen FARC, sun fara wani taron sasantawa da kuma samun zaman lafiya a kasar Norway.Wannan matakin, wani yunkuri ne na kawo karshen tashin hankalin da aka shafe shekaru 50 ana yi.Wannan taron da gwamantocin kasashen Norway da Cuba ke shiga tsakani, shine karo na hudu da ake kokarin sasanta bangarorin biyu,Yayin da ake gudanar da taron, shugaban kasar Colombia, Juan Manuel Santos, yace ba zasu tsagaita wuta ba, saboda kar a shammace su, ganin cewar an fuskanci irin wannan matsala a baya.Sau uku a baya gwamnatin kasar a karkashin shugaba Belisario Betancur, Cesar Gaviria da Andres Pastrana suna kokarin sasantawa amma ana kasa samun biyan bukata.Muhimman batutuwan da bangarorin zasu amince da su, sun hada da bunkasa yankuan karkara na Yankunan ‘yan Tawayen, barin Yan Tawayen su kafa Jam’iya ta kansu, shirin Gwamnatin na magance matsalar nomawa da kuma sarrafa miyagun kwayoyi, abin da ke samawa ‘yan Tawaye kudade, kafa hukumar sasanta ’yan kasar, don binciko yadda aka kashe mutane 600,000, da kuma tilastawa miliyan uku da dubu dari bakwai gudun hijira. 

Shugaban Colmbiya Juan Manuel Santos
Shugaban Colmbiya Juan Manuel Santos © Reuters
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.