Shugaban Nigeria Jonathan ya gana dana Faransa Sarkozy
Shugaban Nigeria Goodluck Jonathan dake ziyarar aiki ta kwanaki uku a kasar Faransa, ya gana da mai masaukinsa Nicolas Sarkozy, inda kasashen suka tattauna hanyoyin da zasu bunkasa hulda dake tsakani.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Tunda fari kasashen biyu sun bayyana cimma matsaya inda Faransa zata baiwa Nigeria bashin kudaden da suka kai Dala milyan 100, wanda bangare ne na Dala milyan 330, domin bunkasa sufuri a birnin Lagos cibiyar kasuwancin kasar, wanda ake aikin hadin gwiwar gudanrwa da Bankin Duniya.
Birnin Lagos shine mafi girma tsakanin biranen dake yankin Yammacin Afrika, kuma kasar ta Nigeria ke kan gaba wajen fitar da man fetur zuwa kasashen duniya, tsakanin kasashen dake Nahiyar ta Afrika.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu