Isa ga babban shafi
Turai

Taron Shugabannin Tarayyar Turai kan Matsalolin Kudade

Yau ake bude taron yini biyu a Brussels na Shugabannin kasashen Turai inda zasu tattauna batutuwa da dama, ciki har da batun cusa da'a wajen tafiyar da kasasfin kudaden kasashen.Tun jiya jajibarin fara taron Shugabannin Kungiyar kwadago na kasashen Turai suka so kawo cikas, a harabar helkwatar Kungiyar ta EU inda suka nuna ra'ayin su na kyamar matakan tsuke bakin aljihu.

Getty Images/Shaun Egan
Talla

Shugabannin kungiyoyin kwadagon sama da 200, sun yi ta nuna rubuce-rubuce dake cewa bama son matakan tsuke bakin aljihu, wasu kuma na cewa akawar da matakan tada komadan tattalin arziki.

A karo na farko dai kungiyar kwadagon ta yi nasaran shirya irin wannan ‘yar kwarya-kwaryar bore a duk kasashen dake cikin kungiyar Turai.

Cikin abubuwan da ake saran taron Shugabannin kasashebn na Turai zai tattauna akwai batun sanya hannu cikin yarjejeniyar tsarin kasafin kudade, da watakila dana kara nada Herman Van Rompuy a matsayin Shugaban kungiyar kasashen masu amfani da kudaden Euro baya ga Shugabancin Hukumar kasashen Turai.
 

Ana saran har ila yau zasu tattauna batun shigar kasar Sabiya cikin kungiyar
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.