Isa ga babban shafi
EU

Tarayyar Turai ta janye jakadu daga Belarus

Kungiyar Kasashen Turai ta janye daukacin Jakadun ta daga kasar Belarus, dan maida martani kan yadda kasar ta kori Jakadun ta guda biyu, bayan sanyawa kasar takunkumi.

REUTERS/Vasily Fedosenko
Talla

Babbar jami’ar diplomasiyar kungiyar, Catherine Ashton, ta ce sun dauki matakin ne dan nuna goyan baya ga Jakadun guda biyu na Poland da kungiyar kasashenTurai da aka kora.

Tuni Taryyar ta Turai ta saka takunkumi kan manyan jami'an Belarus 160, yayin da kasar Amurka ta ce mahukuntan Minsk suna kara mayar da kansu saniyar ware, kuma zasu dandana kudarsu kan abunda suka aikata.

Mahukuntan kasra ta Belarus sun cafke mutane masu yawa bayan zanga zangar zargin magudin zaben shekara ta 2010.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.