Isa ga babban shafi
EU-Masar

Shugabannin kasashen Faransa da Jamus sun bukaci sa Baki da gaggawa ga rikicin kasar Masar

Shugaban kasar Faransa Fracois Hollande da shugabar gwamnatin kasar Jamus Angela Markel sun bukaci yankin kasashen Turai da su yi gaggawar kiran taron tattaunawa domin sa Baki ga yanda rikicin Siyasar kasar Masar ke ci gaba da watsuwa a sauran biranen kasar.

Wani wurin da aka kai hari a masar.
Wani wurin da aka kai hari a masar.
Talla

An dai bayyana cewar shugabannin kasashen biyu duka sun tattauna ne kan wannan batun ta Wayar Tarho, inda suka bukaci a yi gaggawar ganin karshen rikicin tun bai kai kasar ga shiga wani hali ba.

Shugaba Hollande wanda aka bayyana cewar na shirin ganawa da Priministan kasar Ingila David Cameron wani lokaci a yau Jumu’a, ya kira kuma sun tattauna akan wannan matsalar.

Daga cikin abubuwan da wadannan shugabannin ke bukata dai shi ne tabbatar da ganin Ministocin harkokin wajen kasashen sun hadu a cikin gaggawa a Sati mai zuwa domin daukar matakin goyon bayan gwamnatin kasar Masar domin magance watsuwar rikicin, tare da samar da tsayawa akan matsayi guda.

Dubban mutane ne dai aka bayyana cewar sun fito domin yin zanga-zanga a biranen kasar ta Masar domin ci gaba da nuna rashin amincewar su da matakin da Sojin kasar ke dauka akan su.

Kungiyar tarayar Turai dai ta bayyana cewar wani lokaci a Ranar Litinin ne mambobinta ke shirin haduwa domin yin bitar rikicin kasra ta Masar inda ayukan Soji suka kai ga mutuwar akalla Darruwan mutane.

Akalla dai an bayyana cewar an hallaka mutane sun fi Dari shida bayan tashin jerin zanga-zangogi da aka kwashe kusan Wata Biyu na gudanarwa.

Ko a yau Jumu'a dai an bayyana cewar an kashe akalla mutane 41 a Masallacin Dandalin Ramses da ke a birnin Cairo na kasar ta Masar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.