Isa ga babban shafi
Ukraine

‘Yan kishin Rasha sun kakkabo Jiragen Ukraine

‘Yan tawayen Ukraine da ke kishin sun kakkabo Jiragen Ukraine masu saukar Ungulu tare da kashe matuka jiragen guda biyu, a yayin da suke ci gaba da rike ikon birnin Slavyansk. Gwamnatin Ukraine tace tana ci gaba da tunkarar ‘Yan tawayen a gabacin Ukraine.

Jirgin ukraine mai saukar Ungulu
Jirgin ukraine mai saukar Ungulu REUTERS/Gleb Garanich
Talla

Ma’aikatar cikin gida a Ukraine tace akwai mutane da suka jikkata amma sun karbe ikon shingen binciken ‘Yan tawaye guda Tara.

Slovyansk na cikin manyan biranen Ukraine da ke ikon ‘Yan tawaye da ke neman ballewa daga kasar.

An shafe makwanni Dakarun Ukraine na fafatawa da ‘Yan tawayen a sassan gabacin kasar da suka karbe.

Gwamnatin Ukraine da kasashen Yammaci suna zargin Rasha da marawa ‘Yan tawayen baya kamar yadda ta faru da Crimea da ta koma ikon Rasha.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.