Isa ga babban shafi
Ukraine

Shugaban Ukraine zai tarwatsa ‘Yan tawaye

Zababben Shugaban kasar Ukraine Petro Poroshenko ya lashi takobin hukunta tarwatsa ‘yan tawaye masu goyon bayan kasar Rasha, da suka kakkabo wani jirgin soja mai saukar ungulu, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 12.

Sojan Ukraine suna  musayar wuta da 'Yan tawaye a Donetsk.
Sojan Ukraine suna musayar wuta da 'Yan tawaye a Donetsk. REUTERS/Yannis Behrakis
Talla

Wannan ne harin da ya fi kowanne muni tun bayan fara boren neman ballewa daga kasar, lamarin da ya sa fadar gwamnatin Amurka ta White House tace ‘yan tawayen suna samun tallafi daga waje.

An yi amfani ne da manyan makamai wajen kakkabo jirgin daga kasa, kuma yau ministan tsaron kasar ta Ukraine, Mykhailo Koval zai bayar da cikakkakun bayanai kan lamarin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.