Isa ga babban shafi
Ukraine

An kai mummunan hari a filin jirgin sama na kasar Ukraine

An kai mummunan hari a babban filin jirgin saman Donesk na kasra Ukraine a yayin da Dakarun kasar Ukraine ke fada da ‘yan tawaye masu goyon bayan kasar Rasha. Wannan lamarin ya dada zafafa tashin hankalin da ake samu a kasar ta Ukraine.Akalla Sa’oi 4 ne aka kwashe ana tafka kazamin fada da muggan makamai tare da jefa Boma Bomai a babban filin jirgin Donesk, lokacin da Dakarun Gwamnati ke fada da ‘yan tawaye masu ci gaba da rike wasu muhimman Cibiyoyin Sufuri a yankin Gabashin kasar ta Ukraine.Wannan na zuwa ne a yayin da Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry, ke bayyana shirin Amurkar na goyon bayan sabuwar Gwamnatin da za’a kafa a Uklraine, bayan bayyana Petro Poroshenko a matsayin wanda ya samu nasarar lashe zaben da aka gudanar a karshen makon day a gabata.An dai bayyana zaben da aka gudanar a ranar Lahadin data gabata a matsayin muhimmi a tarihin kasar, wadda Mamba ce a tsohuwar tarayyar Soviet, kuma yanzu haka tana kokarin tsayuwa da kafafunta bayan kwashe watanni ana bata-kashi a kasar.An gudanar da zaben na Ukraine cikin nasara, kuma hakan ya kara fito da kokarin da kasar ke yi na komawa a kan tirbar Dimokradiyya.Matsayin da kasar Rasha ta dauka dangane da kasar Ukraine, da kuma matakan karya tattalin arzikin kasar Rasha, da suke kallo a matsayin mai kokarin yiwa Ukraine katsalanda, ya kara rura Wutar rikicin da ya lakume rayukan mutane da dama. 

Wurinda aka yi gumurzu a birnin Donetsk na kasar Ukraine
Wurinda aka yi gumurzu a birnin Donetsk na kasar Ukraine REUTERS/Yannis Behrakis
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.