Isa ga babban shafi
Faransa

Mutane 128 ne suka mutu a harin ta'addancin birnin Paris

A birnin Paris na Faransa akalla mutane 128 ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu 180 ke suka samu munanan raunuka sakamakon hare-haren ta’addancin da ake kai wa birnin a cikin daren juma’ar da ta gabata.

Jami'an tsaro a Bataclan, Paris, 13 ga watan disambar 2015
Jami'an tsaro a Bataclan, Paris, 13 ga watan disambar 2015 REUTERS
Talla

 

  Da farko dai wasu ‘yan bindiga uku ne suka kutsa kai a cikin wani fili inda ake wasan sada zumunci tsakanin Faransa da Jamuskuma shugaban Francois Hollande na daya daga cikin ‘yan kallo a filin.

Jim kadan bayan haka ne wasu ‘yan bindiga hudu suka kutsa kai a cikin wani gidan wasa da ake kira Bataclan inda a can kawai aka samu asarar rayukan mutane akalla 80.

Bayanai sun ce ‘yan bindigar sun yi kokarin yin garkuwa da dubban mutane da ke cikin zauren, kafin daga bisani su yi musayar wuta tsakaninsu da jami’an tsaro daga nan kuma suka tarwatsa kansu.

Shugaban Faransa Francois Hollande ya ayyaka kafa dokar ta baci a kasar, yayin da aka bayar da umurnin rufe iyakokin kasar baki daya. Binciken farko ya tabbatar da cewa yawan maharan zai kai 8, kuma dukkaninsu an kashe su.

Hare-haren dai sun faru ne a wuraren a ba su da nisa da juna a birnin, lamarin da ya tilasta wa shugaban Hollande kiran taron gaggauwa na majalisar ministocir a cikin daren jiya, tare da kai ziyara a wasu daga cikin wuraren da aka kai wa harin.

A yau asabar kuwa shugaban zai jagoranci taron majalisar tsaron kasar, tare da duba sabbin matakai domin kare kasar.

Kawo yanzu dai ba wata kungiya da ta ta fito ta dauki alhakin kai hare-haren, yayin da manazarta ke danganta lamarin da irin rawar da kasar ke takawa wajen fada da ayyukan ta’addanci a kasashen duniya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.