Isa ga babban shafi
Ukraine-Rasha

Ukraine ta karrama Savchenko bayan Rasha ta sake ta

Gwamnatin Ukraine ta karrama direbar jirgin sojin saman kasar, Nadiya Savchenko da babbar lambar yabo bayan hukumomin Rasha sun sake ta a yau Laraba.

Nadiya Savchenko tare da shugaban kasar Ukraine, Petro Poroshenko
Nadiya Savchenko tare da shugaban kasar Ukraine, Petro Poroshenko REUTERS/Valentyn Ogirenko
Talla

Savchenko ta shafe kusan shekaru biyu kulle a gidan yarin Ukraine yayin da kasashen biyu suka yi musayar fursunoni a tsakaninsu.

Rasha ta saki Nadiya Savchenko mai shekaru 35 a karkashin tsarin musayar fursunoni tsakanin kasashen biyu, inda rahotanni suka ce, ita ma Ukraine din ta saki sojojin Rasha guda biyu.

Jim kadan da isarta Ukraine, Savchenko ta ce, a shirye take ta sake bai wa kasarta gudun mawa a filin daga.

Direbar ta isa Ukraine ne a jargin saman shugaban kasa ba tare da takalami a kafarta ba, amma ta sanya farar riga dauke da alamar kasarta kuma daga nan ne aka garzaya da ita fadar shugaban kasar Petro Poroshenko, inda ya karrama ta da babbar lambar girmamawa ta kasar.

Shugaba Poroshenko ya yi alkawarin cewa, Ukraine za ta karbe ikon yankin Crimea wanda Rasha ta mamaye shekaru biyu da suka gabata kuma shi ne yankin da ‘yan tawaye ke rike da shi .

A cewar shugaban, za su dawo da Donbas da Crimea da ke gabashin kasar kamar yadda suka dawo da Nadiya Savchenko wadda ta shafe tsawon kwanaki 709 a karkashin garkuwar Rasha.

Savchenko dai ta bukaci al’ummar Ukraine da su tashi tsaye domin neman hakkinsu daga wadanda ke tauye su kuma ana ganin kalamanta shagube ne ga shugaba Vladmir Putin na Rasha.

A lokacin da take tsare a hannun hukumomin Rasha, Nadiya Savchenko ta sha shiga yajin kin cin abinci da shan ruwa domin nuna bore ga matakin tsare ta a gidan yari.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.