An dage taron sasanta rikicin Syria
Jakadan Majalisar Dinkin Duniya kan sasanta rikicin kasar Syria Staffan de Mistura ya ce an dage taron da aka shirya yi ranar 8 ga wannan watan na Fabairu zuwa ranar 20 don bai wa bangaren 'yan adawa damar sasanta tsakaninsu.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Jami’in wanda ke yi wa Majalisar Dinkin Duniya bayani ya ce an dauki matakin ne dan bai wa bangarorin ‘yan adawan kasar damar shiryawa a tsakanin su.
Kasashen Rasha da Turkiya da Iran sun jagoranci wani taro a makon jiya a birnin Astana da ke kasar Kazakhstan dan ganin an samo hanyar kawo karshen rikicin da ya lakume rayukan mutane sama da 310,000 yanzu haka.
Shekaru fiye da biyar kenan ake yaki a Syria, yakin da ya ki ci ya ki cinyewa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu