Yanzu haka dai sakamakon dindindin na zaben shugabancin Faransa da aka gudanar zagaye na farko, ya tabbatar da cewa Emanuel Macron dan takarar tsakiya mai zaman kansa ne ke kan gaba da kusan kashi 24 cikin 100, yayin da uwargida Marine le Pen ta jam’iyar masu tsatsauran ra’ayin ke biye masa, da kashi 21 na kuri’un da aka kada.
Talla
To domin jin yadda masharhanta a nahiyar Afrika ke kallon wannan zabe da kuma tasirinsa ga nahiyar, Mahaman Salisu Hamisu ya tattauna da Farfessa Ado Mahaman daga Jamhuriyar Nijar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu