Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa zata zuba euro miliyan 100 don samar da man hydrogen

Faransa ta kaddamar da shirin bunkasa samar da sinadarin hydrogen domin bada damar fara amfani da shi a matsayin makamashi a masana’antu da kuma fannin sufuri.

Ministan Muhalli na Faransa, Nicolas Hulot.
Ministan Muhalli na Faransa, Nicolas Hulot. REUTERS/Charles Platiau
Talla

Ministan muhalli na kasar Nicolas Hulot ne ya bayyana haka, yayin ganawa da wakilan masana’tun kasar ta Faransa, inda ya ce gwamnati zata zuba jarin euro miliyan 100 a shekara mai zuwa domin cimma wannan buri.

Ministan muhallin ya ce shirin ya tsara samar da akalla ababen hawa na haya 5,200 masu amfani da sinadarin na Hydrogen a madadin fetur, wadanda suka hada da motocin safa, jiragen kasa da kuma motocin dakon kaya nan da zuwa shekara ta 2023, idan aka kwatanta da ababen hawan na haya masu amfani da sinadarin na hydrogen guda 260 da ke aiki a Faransar a yanzu.

Zalika za a gina sabbin gidajen samar da man na sinadarin Hydrogen guda 100, kari akan 20 da aiki a yanzu.

Tuni dai kasar Jamus ta yi nisa akan shirin na maye gurbin man fetur da sinadarin hydrogen, inda a yanzu ta ke da gidajen da ke bada man sinadarin na hydrogen guda 100.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.