Isa ga babban shafi
Tattalin arziki

Bankin Societe Generale na Faransa zai biya tarar Dala biliyan 1,34

Bakin Societe Generale na Faransa ya amince ya biya tarar Dala biliyan 1,34 domin kawo karshen wani cece-ku-ce da ke tsakaninsa da da kasashen Amurka da Faransa da suka danganci badakala ta kudaden ruwa da kuma zargin bada cin hanci a kasar Libiya.

Kudin Euro na Faransa
Kudin Euro na Faransa
Talla

Yanzu haka dai bankin na S G zai zuba kimanin miliyan 860 na dalar Amurka ga Bankin Doj da ke birnin New York kan badakalar kudaden ruwa da kuma rufe binciken da ake yi masa kan bayar da cin hanci ga wani dillalin kasar Libiya a tsakanin 2004 da 2009, domin hukumar zuba jarin kasar Libiya wato Libyan Investment Authority LIA ta zabi bankin na SG a matsayin wanda zai ci gaba da bata shawarwari da kuma ajiye kudaden hannayen jarinta da ke ketare.

A gaba daya dai, Société Générale ya zuba miliyan 90 na dalar Amurka ne ga dillalin da mafi yawan kudaden aka dankasu ga hannun wasu manyan mahukumtan kasar Libiya domin samun yin hulda da maáikatu da hukumomi da dama na kasar ta Libiya, kamar yadda gwamnatin Amurka ta sanar.

Mai gabatar da kara kan harkokin da suka shafi bankuna a Faransa ya ce bankin ya amince ya biya Faransa tarar euro miliyan 250, ita ma Amurka miliyan 500 domin kaucewa binciken sa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.