Isa ga babban shafi
Majalisar Dinkin Duniya

China, Rasha sun yi fatali da kudirin tsagaita wuta a Syria

Kasashen Rasha da China, sun hau kujerar naki, kan kudurin kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya, na umarnin tsagaita wutar yaki a lardin Idlib na Syria.

António Guterres, Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya
António Guterres, Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya REUTERS/Brendan McDermid
Talla

Kudurin da Jamus, Belgium da kuma Kuwaiti suka gabatar da fari ya samu goyon 12 daga cikin kasashe 15 masu kujerar din-din-din a zauren kwamitin sulhun.

Rasha da China sun hau kujerar nakin ne biyo bayan bukatar wasu kasashe da suka hada da Jamus, Belgium da Kuwait da suka bukaci a tsagaita wuta a yankin Idleb, matakin da wakilan kasashe 123 suka amince da shi.

Wannan dai ne karo na 13 da kasar Rasha ke hawan kujerar naki dangane da batun Syria tun bayan da yakin Syria ya barke a shekara ta 2011, yayin da kasar Equatorial Guinea da ke a matsayin yar kallo ta kasance yar ba ruwan mu.

Jakadan Rasha a majalisar Dinkin Duniya Vassily Nebenzia a lokacin kare matakin da Rasha ta dau jakadan na Rasha ya bayyana cewa, kaucewa yin na’am da wannan zance da Rasha ta yi na da matukar tasiri, wasu daga cikin matsalolin da aka fuskanta a baya sun hada da yawaita hare –hare daga yan ta’ada da ke canza kansu zuwa wakilan yan adawa.

Rahotanni daga wata majiyar diflomasiya na nuni cewa za a ci gaba da kai wasu jerrin hare-hare ta sama a yankin Idlib, wanda hakan ke zuwa watanni hudu bayan da rundunar sojin Syria karkashin gwamnatin Bashar al Assad ta kaddamar da hare-hare ta sama zuwa yankin na Idlib da ke dauke da kusan milyan uku na jama’a da kusan yara milyan daya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.