Isa ga babban shafi
Faransa-Coronavirus

Coronavirus: Yawan jariran da ake haifa a Faransa ya ragu da kashi 13 cikin 100

Ma’aikatar kididdiga a Faransa tace yawan jariran da ake haihuwa a kasar ya ragu da kashi 13 cikin 100 cikin watan Janairun da ya gabata.

Wasu ma'aurata tare da jaririnsu sabon haihuwa a wani asibiti dake birnin Paris, yayin da ake fama da barkewar annobar Coronavirus a Faransa. 17/11/2020.
Wasu ma'aurata tare da jaririnsu sabon haihuwa a wani asibiti dake birnin Paris, yayin da ake fama da barkewar annobar Coronavirus a Faransa. 17/11/2020. AFP - MARTIN BUREAU
Talla

Raguwar adadin jariran da ake haifa a Faransar na baya bayan nan dai shi ne koma baya mafi girma da kasar ta gani cikin shekaru 45.

Sabbin alkaluma sun nuna cewar, jarirai dubu 53 da 900 aka haifa a Janairun wannan shekara, sabanin dubu 62, 180 a Janairun shekarar 2020.

Ma’aikatar kididdigar ta Faransa ta alakanta lamarin da tasirin annobar Korona, da ta tilastawa iyalai da dama dage shirinsu na neman haihuwa, har zuwa lokacin da za a shawo kan cutar ta Korona.

Cikin shekarar bara ta 2020, alkaluma suka nuna raguwar jariran da ake haihuwa duk shekara a Faransa zuwa dubu 735, koma baya mafi girma tun bayan yakin duniya na 2.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.