Isa ga babban shafi
Faransa-Coronavirus

Allurar rigakafi 1 kawai za a yiwa wadanda suka warke daga Korona - Faransa

Faransa ta zama kasa ta farko da ta baiwa hukumomin lafiyar ta umarnin yin allurar rigakafin Korona sau daya ga wadanda suka warke daga cutar a maimakon sau biyu.

Wata Bafaranshiya yayin karbar allurar rigakafin cutar Korona a yankin Loos, dake arewacin Faransa. 28/12/2020.
Wata Bafaranshiya yayin karbar allurar rigakafin cutar Korona a yankin Loos, dake arewacin Faransa. 28/12/2020. Francois Lo Presti/AFP
Talla

A cewar gwamnatin Faransar kwararru sun tabbatar mata marasa lafiyar da suka warke daga cutar ta Korona na samun kariyar da tayi dai dai da allurar rigakafi daya, dan haka yi musu allurar guda-guda ya wadatar.

Zalika aiwatar da tsarin zai taimaka wajen samun rarar maganin cutar ta Korona,la'akari da yiwuwar karuwar masu bukatar sa.

Dukkanin alluran rigakafin Korona na Pfizer da BioNTech, Moderna da kuma AstraZeneca baiwa mutane sau bibbiyu ne a kasashen kungiyar tarayyar Turai, saboda binciken da ya nuna wadanda suka samu sau biyu sun fi samun Kariya daga annobar sama da wadanda suka samu sau daya.

Zuwa ranar Alhamis da ta gabata, kididdiga ta nuna cewar sama da mutane miliyan 2 da dubu 100 sun samu allurar rigakafin cutar Korona sau guda a Faransa, yayin da wasu kusan dubu 535, da 800 suka samu alluran kashi biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.